Gwamnatin tarayya ta mika kayan dafa abinci kimanin dubu 150 ga gwamnatin jihar Jigawa

0 84

Gwamnatin tarayya ta hannun ma’aikatar jin kai da kula da annoba ta mika kayan dafa abinci kimanin dubu 150 ga gwamnatin jihar Jigawa domin wadanda suka ci gajiyar shirin ciyar da daliban makaranta.

Ministar jin kai da kula da annoba, Sadiya Umar-Farouq wacce babban sakatare a ma’aikatar, Bashir Nura Alkali ya wakilta, ta bayyana hakan jiya yayin mika kayayyakin ga gwamnatin jihar Jigawa.

Ta ce an tsara shirin ne don magance talauci ta kowane fanni tare da hadin gwiwar jihohi.

Ta ce a karkashin shirin gwamnatin tarayya ta ciyar da dalibai sama da miliyan 9 tare da daukar masu dafa abinci sama da dubu 100 a fadin kasar nan.

A jihar Jigawa kadai, ta ce shirin ciyarwar yana gudana a makarantun firamare dubu 2 da 180, wanda ya kunshi dalibai dubu 490 da 874, da masu dafa abinci dubu 5 da 267 a Kananan Hukumomi 27 dake fadin jiharnan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: