Gwamnatin Najeriya ta musanta rahotannin da ke nuna cewa tana da aniyar ƙara kuɗin wutar lantarki cikin watanni masu zuwa.
A cikin wata sanarwa da ta fitar, mai bai wa shugaban Najeriya, Bola Tinubu shawara kan makamashi, Olu Arowolo Verheijen, wadda aka ruwaito tana cewa cewa “za a yi ƙarin kashi 65 na kuɗin”, ta ce an yi wa kalamanta gurguwar fassara.
Jami’ar dai ta yi wannan kalami ne a taron makamashi na Afirka da aka gudanar a birnin Dar es Salam na ƙasar Tanzaniya, inda jaridun Najeriya da dama suka wallafa batun.
Ta ce bayan ƙara kuɗin wutar na Band A a shekarar 2024, a yanzu kuɗin da ake samu daga wutar lantarkin ya na biyan kashi 65 ne cikin kuɗin da ake kashewa wurin samar da wutar, inda gwamatin ƙasar ke cigaba da biyan giɓin da ake samu.
Olu Verheijen ta kuma ce duk da dai gwamnatin ta duƙufa wajen samar da kuɗin wuta mai sauƙi nan gaba, abin da ta mayar da hankali kai a yanzu shi ne tabbatar da samar da ƙarin wutar lantarkin ga ƴan ƙasar, da tabbatar da rage ɗaukewar wutar, da kuma tabbatar da kare marasa ƙarfi.
A shekarar 2024 ne gwamnatin Najeriya ta janye wani ɓangare na tallafin lantarki da take biya, lamarin da ya haifar da hauhuwar farashin kuɗin wuta ga masu tsarin ‘Band A’ a faɗin ƙasar.
Lamarin ya janyo ƙorafi a faɗin ƙasar ganin irin halin taɓarɓarewar tattalin arziƙi da al’umma ke fuskanta.