Gwamnatin Tarayya ta nemi ma’aikatu masu zaman kansu da su biya mafi karancin albashi na ₦70,000

0 87

Gwamnatin Tarayya ta yi kira ga hukumomin da ke daukar ma’aikata masu zaman kansu da su bi tsarin mafi karancin albashi na Naira dubu 70, inda ta yi gargadin cewa ba za a amince da duk wani sabani ba.

A cewar Gwamnatin Tarayya, sabon mafi karantar albashin ya zama dole don magance yanayin tattalin arzikin da ake ciki a halin yanzu, inda ta jaddada cewa babu wani ma’aikacin Najeriya, ko yana aikin gwamnati ko na zaman kansa da ya kamata a biya kasa da mafi karancin albashi na Naira dubu 70.

Babban sakataren ma’aikatar kwadago da samar da ayyukan yi, Alhaji Ismaila Abubakar, ne ya bayyana hakan a jiya Larabar, yayin da yake jawabi a wajen taron shekara-shekara na kungiyar ma’aikata na ma’aikatu masu zaman kansu karo na 13, wanda aka gudanar a Ikeja, Legas.

A nata jawabin shugabar kungiyar ta NLC reshen jihar Legas, Funmilayo Sessi, ta ce wahalhalun da ake fama da su ya haifar da rugujewar duk wani kudin shiga da kowane ma’aikaci ke samu a fadin kasar, inda ta yi kira ga ma’aikata masu zaman kansu da su tabbatar da biyan mafi karancin albashi na Naira dubu 70.

Leave a Reply

%d bloggers like this: