Gwamnatin tarayya ta rabar da Naira Biliyan 1 da miliyan 200 ga zababbun mutane a jihar Bauchi

0 83

Gwamnatin tarayya ta rabar da Naira Biliyan 1 da miliyan 200 ga mutanen da aka zaba domin cin gajiyar shirin gwamnatin tarayya na yaki da talauci a Jihar Bauchi.

Shugabar Sashen Horaswa da Sadarwa ta Shirin a Jihar Bauchi Malama Jamila Affan, ita ce ta bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a Bauchi.

A cewarta, Shugaban Shirin Yaki da Talauci na Jihar Bauchi Mallam Jibrin Muhammad Fanti, shine ya bayyana hakan a lokacin da yake kaddamar da rabon a cibiyar bada agajin ta Duguri a karamar hukumar Alkaleri ta Jihar.

Shugaban Shirin ya ce kimanin Mata dubu 54,0721 ne suka samu tallafin Naira dubu N20,000 domin biyan su hakkokin su na watannin Janeru da Afrilu.

Mista Fanti, ya ce an bada Naira dubu N10,000 ga wadanda aka zaba su ci gajiyar shirin bunkasa Ilimin Mata.

Kazalika, ya ce za’a fara aiwatar da shirin tura kudaden ta asusun bankunan mutanen da aka zaba a kananan hukumomin Alkaleri, Kirfi, Dass, Tafawa Balewa, Bogoro, Toro, Ganjuwa, Ningi, Darazo, Dambam, Jama’are, Zaki, Gamawa da Itas Gadau.

Leave a Reply

%d bloggers like this: