Gwamnatin Tarayya ta tattara kayan aiki domin dakile yaduwar cutar kwalara a Najeriya

0 111

Ministan lafiya da walwalan jama’a, Farfesa Muhammad Ali Pate, ya yi kira da a dauki matakai daban-daban don dakile barkewar cututtuka kamar Kwalara, zazzabin Typhoid da tarin fuka.

Ministan lafiya ya kuma ce Gwamnatin Tarayya ta tattara kayan aiki domin dakile yaduwar cutar kwalara a kasar.

Farfesa Pate ya ce an kaddamar da wata kungiya ta kwararru ta Cibiyar Kula da Cututtuka ta kasa (NCDC) don tallafawa jihohi don rage yaduwar cutar da kuma kula da wadanda suka kamu da cutar.

Farfesa Pate ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa za a takaita barkewar cutar kwalara daga yaduwa zuwa wasu jihohi da kananan hukumomi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: