Gwamnatin Tarayya ta umarci da a hanzarta gyara hanyoyin da suka lalace sakamakon ambaliyar ruwa

0 99

Gwamnatin Tarayya ta umarci hukumomin ta su hanzarta gyara hanyoyin da suka lalace sakamakon ambaliyar ruwa a jihohi 5 da suke Kasar nan.

Cikin hanyoyin da suka lalace sun hada da Ibadan – Ife Road, Gombe – Bauchi Road, Gombe – Darazo; Bauchi – Ningi, Bida – Lambata, and Tsamiya bridge in Jigawa State.

Ministan Ma’aikatar Ayyuka da Gidaje Mista Babatunde Raji Fashola ya umarci hukumomin da suke gyaran hanyoyin da suka lalace suyi gaggawar gyara hanyoyin da ambaliyar ruwa ta lalata su a Jihohi 5 na kasar nan.

Ministan ya bayyana hakan ne a taron yiwa manema labarai Jawabi a Abuja, inda ya bada tabbacin mayar da hankali kan hanyoyin da suke da irin wannan matsalar.

A cewarsa, Gwamnatin tarayya ta jajirce wajen bunkasa hanyoyin more rayuwa, tare da karbar korafe-korafen Al’umma.

Kazalika, ya bukaci Matafiya su kasance masu hakuri sakamakon matsalolin da suke fuskantar akan hanyoyin da ambaliya ta lalata su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: