Gwamnatin tarayya ta umarci dukkan kamfanonin sadarwa da su katse masu amfanin da layukan waya matukar ba su yi rajistar NIN ba

0 52

Gwamnatin tarayya ta umarci dukkan kamfanonin sadarwa da ke cikin kasarnan su katse masu amfanin da layukan waya matukar ba su yi rajistar layukan ba, ko kuma ba su hada su da lambar zama dan kasa ba (NIN) daga yau Litinin 4 ga watan Afrilun 2022.

Hukumar da ke kula da harkokin sadarwa ta kasa NCC tare da hukumar da ke kula da kuma yin rajistar ‘yan kasa (NIMC) ne suka bayyana haka a cikin wata sanarwa ta hadin gwuiwa da suka fitar.

Wannan matakin na nufin wadanda aka rufe layukansu saboda rashin hada su da lambar dan kasa ba za su iya kiran kowa ba, sai dai za a iya kiransu.

Ministan sadarwa na kasar Isa Ali Pantami ne ya bayar da umarnin.

Gwamnatin tarayyar ta ce kawo yanzu, ta mika lambobin waya miliyan 125 domin a hada su da lambar dan kasa, kuma hukumar NIMC ta yi rajistar lambobin dan kasa miliyan 78 kawo yanzu.

Wannnan na zuwa ne adaidai lokacin da hukumar sadarwa ta kasa NCC ta tabbatar da cewa yanzu haka akwai kimanin lauyukan waya miliyan 198 da dubu dari 8 da suke aiki a kasar nan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: