

- Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa NAFDAC ta rufe kamfanonin ruwa guda 10 a jihar Ondo bisa rashin bin ka’idoji - July 4, 2022
- Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar AA, Hamza Al-Mustapha, ya ce jam’iyyarsa ba za ta yi hadin gwiwa da mutanen da basu damu da makomar al’umma ba - July 4, 2022
- Yadda wani mutum ya kona matarsa bayan ya gama dukanta a jihar Ogun - July 4, 2022
Ministar harkokin jin kai, kula da annoba da walwalar jama’a, Sadiya Umar Farouq, tace gwamnatin tarayya ta ware kudi naira miliyan dubu 5 da miliyan 900 domin bayar da horo da kayan aiki da alawus-alawus na wata-wata ga masu cin gajiyar shirin N-Power a rukunin C.
Ministar ta sanar da haka a jiya yayin bikin rufe shirin koyar da gyaran waya ga matasa 177 a karkashin shirin N-Power a jihar Kano.
Sadiya Farouq tace yanzu haka matasa 629 ne suke cin gajiyar shirin a jihar, inda kimanin dubu 18 da 42 suke rukunin A da B na shirin.
Sadiya Farouq, wacce ta samu wakilcin mai taimakawa shugaban kasa Muhammadu Buhari na musamman akan sana’o’in hannu, Nasiru Mahmoud, ya shawarci wadanda suka ci gajiyar shirin da kada su sayar da kayan aikin da aka basu.