Gwamnatin Tarayya ta yi gargaɗi ga ‘yan ƙasa akan masu damfara da ke yaɗa labaran bogi na daukar aiki

0 150

Gwamnatin Tarayya ta yi gargaɗi ga ‘yan ƙasa da su guji fadawa tarkon masu damfara da ke yaɗa labaran bogi kan daukar aiki a ma’aikatu karkashin Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida.

Wata sanarwa daga Sakatare na Hukumar Daukar Ma’aikata ta Tsaro, da Gyara, da Kashe Gobara da Shige da Fice, Manjo Janar Abdulmalik Jibril (mai ritaya), ta ce duk da amincewar Shugaban Ƙasa ga daukar ma’aikata, akwai matakai da dama da dole sai an bi kafin fara aikin daukar.

Ya kara da cewa, duk wani shirin daukar ma’aikata za a sanar da shi ta hanyar talla a jaridu na ƙasa tare da tabbatar da gaskiya da adalci ba tare da biyan wani kudi ba. Wannan na zuwa ne bayan wata wasika daga cikin ma’aikatar ta bayyana a kafafen sada zumunta, lamarin da ya tada hankulan matasa da dama da ke neman aiki a Najeriya.

Leave a Reply