Gwamnatin Tarayya tace kungiyar IPOB ta kai hari kan ofishoshin yansanda 164 a jihoshi daban-daban na Najeriya

0 67

Gwamnatin Tarayya tace bincikenta ya nuna cewa ‘yan awaren kungiyar IPOB da aka haramta, ya zuwa yanzu sun kai hari kan ofishoshin yansanda 164 a jihoshi daban-daban.

Gwamnatin tarayya ta kara da cewa ‘yan awaren dauke da makamai sun kashe jumillar jami’an tsaro 175.

Matsayar gwamnatin tarayyar na kunshe cikin wata sanarwa da babban lauyan tarayya kuma ministan shari’ah, Abubakar Malami, SAN ya fitar a yau.

A cewarsa, Gwamnatin tarayyar ta kuma ce wadanda ake zargin yan kungiyar ta IPOB ne sun kaddamar da hare-hare 19 akan gine-gine hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC, lamarin da ya jawo kone motoci 18.

A wani labarin kuma, ‘yan bindigar da ake zargin ‘yan kungiyar IPOB ne, sun cinna wuta kan fadar sarkin kauyen Etekwuru a jihar Imo.

Kazalika, an kone motarsa tare da wasu kayayyaki a lokacin harin.

Majiyoyi sun ce lamarin ya auku a jiya da dare.

Leave a Reply

%d bloggers like this: