Gwamnatin Tarayya tana ɗaukar manyan matakai domin farfaɗo da tattalin arzikin kasar – Mohammed Idris

0 200

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ce Gwamnatin Tarayya tana ɗaukar manyan matakai domin farfaɗo da tattalin arzikin kasar, dawo da ƙwarin gwiwar masu zuba jari, da kuma ƙarfafa dimokiraɗiyya a ƙasar. 

A wata hira ta musamman da ya yi da mujallar Forbes Africa yayin bikin Ranar Dimokiraɗiyya, Ministan ya bayyana cewa manufofin sauyi na Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ciki har da cire tallafin man fetur da daidaita tsarin canjin kuɗi, suna daga cikin manyan sauye-sauye a tarihin tattalin arzikin Nijeriya na baya-bayan nan.

Da yake magana kan muhimmancin bikin Ranar Dimokiraɗiyya ta bana, Idris ya ce wannan ba lokacin murna kaɗai ba ne, har ma lokaci ne na nazari kan cigaban ƙasar wajen ƙarfafa dimokiraɗiyya da farfaɗowar tattalin arziki.

Ya bayyana cewa ana amfani da kuɗaɗen da aka tara daga cire tallafin man fetur wajen gina muhimman ababen more rayuwa, ciki har da manyan tituna guda biyu da za su haura kilomita 1,700, waɗanda za su taimaka wajen bunƙasa harkokin kasuwanci da haɗa yankuna daban-daban.

Ya ƙara da cewa sauye-sauyen da gwamnatin Tinubu ke aiwatarwa ƙarƙashin Shirin Sabunta Fata sun wuce batun tattalin arziki kawai, domin suna gina tushe ne na cigaba mai ɗorewa, raba dama ga kowa, da ƙarfafa gaskiya da riƙon amana.

Leave a Reply