Gwamnatin Tarayya tana shirin samar da ayyukan yi miliyan 21 ta hanyar samar da gine-ginen gwamnati sosai da ayyuka nan da shekaru uku masu zuwa.

Karamin ministan kudi, kasafin kudi da tsare-tsaren kasa, Clem Agba, shine ya fadi haka jiya a Abuja a wajen taron karawa juna sani na kwanaki 5.

Hukumar cigaban tarayyar Afirka da wata kungiyar cigaban Afirka ne suka hada taron.

Yace matakin samar da ayyukan yi miliyan 21 na daya daga cikin makomar shirin cigaban kasarnan wanda yake neman fitar da mutane miliyan 35 daga kangin talauci nan da shekarar 2025.

Yace wannan zai kafa danbar cika alkawarin gwamnati mai ci na fitar da mutane miliyan 100 daga kangin talauci daga nan zuwa shekarar 2032.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: