Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Biyan Kudaden Karin Albashin Ma’aikata A Karshen Wannan Watan

0 161

Matukar ba wani sauyi aka samu a kurarren lokaci ba, Gwamnatin Tarayya za ta fara biyan kudaden karin albashin ma’aikatan gwamnati a karshen wannan watan.

Ana sa ran shugaban kasa Muhammadu Buhari zai bayar da amincewar sa ta karshe na karin albashin kowane daga yanzu.

Idan shirin da aka yi ya samu sahalewa, yana nufin karin zai zo ne kimanin watanni biyu kafin watan Yunin da aka ba da shawarar cire tallafin man fetur.

Jami’an gwamnatin tarayya sun shaida wa manema labarai cewa sabon karin albashi da aka yi wa lakabin karin alawus-alawus, zai haifar da karin kashi 40 cikin 100 na albashin ma’aikatan gwamnati bisa yadda yake a halin yanzu. Da yake jawabi na musamman ga manema labarai, Daraktan Yada Labarai da Hulda da Jama’a na Ma’aikatar Kwadago da Aikin Yi, Olajide Oshundun, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya na iya fara biyan karin albashin kashi 40 cikin 100 a karshen watan Afrilun bana, inda ya kara da cewa za a biya bashin na watanni ukun da suka gabata na Janairu da Fabrairu da Maris a wata ranar nan gaba.

Leave a Reply