Gwamnatin Tarayya Zata Karbi Bakuncin Taron Matasa Na Kungiyar Commonwealth

0 73

Gwamnatin tarayya ta yi alkawarin magance tare da aiwatar da shirye-shiryen ci gaba da ke tasiri kai tsaye ga matasan Najeriya.

Ministan matasa da ci gaban wasanni, Mista Sunday Dare ne, ya yi wannan alkawarin a wajen rufe taron matasa da dalibai na Commonwealth na bana a yankin Afrika da aka gudanar a Abuja.

Ya ce, batutuwan da suka shafi ciyar da matasa gaba, wadanda aka tabo a taron kasa da kasa na mako guda, lamari ne mai bangarori da dama da ke bukatar tsarin da ya shafi bangarori daban-daban domin babu wata hukuma da za ta iya magance kalubalen da matasa ke fuskanta a kowace kasa ba tare da yin magana ba, musamman a Afirka.

Sunday Dare ya ce gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari a cikin wadannan shekaru ta bullo da aiwatar da tsare-tsare da ayyuka daban-daban domin dakile zaman kashe wando da matasa ke yi ta hanyar sanya su cikin sana’o’i masu ma’ana da amfani, wadanda suka taimaka wajen bunkasa zamantakewa da tattalin arziki da ci gaban kasa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: