Gwamnatin Tarayyar ta fara sayar da shinkafa a farashin Naira 40,000

0 122

Gwamnatin Tarayyar ta fara sayar da tan dubu 30,000 na shinkafa a farashi mai rahusa a kan Naira  dubu 40,000 kan wane buhu mai nauyin kilogiram 50.

Ministan Noma, Sanata Abubakar Kyari, ne ya ƙaddamar da wannan shirin a ranar Alhamis a Abuja. 

Ya jaddada cewa raba shinkafar yana gudana a fadin ƙasar nan don magance ƙalubalen tattalin arziki da ke shafar ‘ƙasar nan.

Kyari ya bayyana cewa wannan tallafin abincin umarni ne da shugaban kasa Bola Tinubu don tabbatar da cewa ‘yan ƙasar basa jin yunwa a wannan lokacin rikicin farashin kayan abinci na duniya, bayan annobar COVID-19, da yaƙin Rasha da Ukraine, da canjin yanayi suka haddasa. 

Ya kuma tabbatar da cewa an samar da matakan da za su tabbatar da gaskiya da daidaito wajen raba shinkafar.

Gwamnati ta aiwatar da tsari na tabbatar da wanda zai sayi shinkafar mai tsauri don hana sayen sama da  buhu daya da kuma tabbatar da kowa ya samu daidai, inda za a buƙaci masu sayen su yi amfani da Lambar shaidar ɗan ƙasa (NIN) da lambar wayarsu. 

Kyari ya roƙi ‘yan ƙasa da su haɗa kai da hukumomin gwamnati da ke kula da wannan aikin don tabbatar da nasarar sa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: