Gwamnatin Tarayyata ta amincewa yan kasashen waje su 286 su zama ‘yan Najeriya daga cikin mutane 600 da suka nema

0 68

Majalisar zartaswa ta tarayya ta amincewa ‘yan kasashen waje su 286 su zama ‘yan Najeriya daga cikin mutane 600 da suka nemi hakan.

Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola ne ya bayyana hakan a yau bayan taron majalisar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta.

A cewarsa, adadin wadanda aka tabbatar da amincewa su zama ‘yan kasa sun kai 208, yayin da masu neman hakan su 78 aka amince da su ta hanyar rajista.

Masu neman zama ‘yan Najeriya sun fito daga kowane yanki na duniya da suka hada da Turawa da Amurkawa, da sauran su, kuma hukumomi irin su hukumar tsaro ta farin kaya DSS da ma’aikatar harkokin kasashen waje da hukumar shige da fice ta kasa immigration da kuma gwamnatocin jihoshin da mutanen suke zaune, sun gudanar da bincike sosai akan su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: