Gwamnatin Tinubu na jefa talakawa cikin mawuyacin hali – Atiku

0 151

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar ya zargi gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da fifita masu hannu da shuni yayin da take jefa talakawa cikin mawuyacin hali, yana mai bayyana gwamnatin a matsayin ɗaya daga cikin mafi rashin kwarewa, mai tazarce da kuma maras damuwa da halin jama’a a tarihin dimokuraɗiyyar Najeriya.

A cikin wata sanarwa da ta yi nazari kan shekaru biyu na mulkin Tinubu, Atiku ya ce babu wata gwamnati a baya da ta jefa talakawa cikin irin wannan kuncin rayuwa, tana mai watsi da gaskiya, bayyananniyar shugabanci da kuma ɗabi’ar amana.

Ya ƙara da cewa, baya ga kasancewar Najeriya “babban birnin talauci” a duniya, yanzu haka ƙasar ta zarce Sudan mai fama da yaƙi wajen yawan yara masu fama da rashin abinci, yana mai tawassali da rahoton alkaluman yunwa na duniya na 2024 suka nuna, wanda ya nuna Najeriya a matsayi na 18 cikin ƙasashen da yunwa da rashin abinci suka fi shafa. Tsohon mataimakin shugaban ƙasan ya kuma soki ƙarin kuɗin rajista na Hukumar Kula da Shaidar Ƙasa (NIMC) da na jami’o’in gwamnati a matsayin matakai da ke ƙara ɗora wa talakawa kaya, yana mai jan kunne cewa ‘yan adawa ba za su amince da duk wani yunƙuri na maida Najeriya ƙasa ta jam’iyya ɗaya ba, inda ana murƙushe masu suka da kuma cin zarafin ikon gwamnati.

Leave a Reply