Gwamnatin Zamfara ta bullo da tsarin da zai koyar da ‘yan jihar ƙwarewar fasahar zamani

0 160

Jihar Zamfara ta zama jiha ta farko a kasar nan da ta bullo da tsarin Zamfara Digital Learning Framework (ZDLF), wanda aka ƙirƙira don koya wa al’umma ƙwarewar zamani da za su taimaka wajen bunƙasa tattalin arziki, ƙarfafa shugabanci da haɓaka kirkire-kirkire. 

A ranar Laraba ne aka gudanar da babban taron masu ruwa da tsaki a ɗakin taro na Garba Nadama da ke Gusau, inda manyan masu ruwa da tsaki suka hallara domin tsara hanya mafi nagarta don aiwatar da tsarin. 

Kakakin gwamnan jihar, Sulaiman Bala Idris, ya bayyana cewa taron ya haɗa da wakilan cibiyoyin gwamnatin tarayya, abokan hulɗa na ƙasa da ƙetare, malamai da ‘yan kasuwa masu zaman kansu. 

Wannan yunƙuri ya nuna jajircewar jihar wajen canja fasalin ilimi da shugabanci ta hanyar amfani da fasahar zamani.

Leave a Reply