Gwamnoni 9 zasu halarci taron editocin Najeriya karo na 17 wanda za a fara daga ranar Alhamis a Abuja

0 114

Gwamnoni 9 zasu halarci taron editocin Najeriya karo na 17 wanda za a fara daga ranar Alhamis a Abuja.

Gwamnonin sune Ifeanyi Okowa na jihar Delta; Nasiru El-Rufai na jihar Kaduna; Yahaya Bello na jihar Kogi; Seyi Mankide na jihar Oyo; Bello Matawalle na jihar Zamfara; Babagana Zulum na jihar Borno; David Umahi na jihar Ebonyi; Rotimi Akeredolu na jihar Ondo da kuma Adegboyega Oyetola na jihar Osun.

Kazalika ana saran halartar Ministan tsaro, Bashir Magashi, da ministan ayyuka, Babatunde Fashola, da Babban Hafsan Tsaro, Lucky Irabor da babban mai bawa shugaban kasa shawara kan tsaro, Babagana Monguno, da shugaban kamfanin mai na kasa NNPC, Mele Kyari, da sauransu.

Wata sanarwa a jiya dauke da sa hannun shugaban kungiyar editocin Najeriya, Mustapha Isah, da janar sakatare na kungiyar, Iyobosa Uwugiaren, tace taron zai mayar da hankali kan rashin tsaro a kasarnan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: