Gwamnonin Jam’iyyar APC sun bukaci gwamna Mai Mala Buni da ya gaggauta gudanar da taronsu na kasa

0 87

Gwamnonin Jam’iyyar APC mai mulki sun bukaci gwamna Mai Mala Buni da ke jagorancin kwamitin rikon kwaryar da ke tafiyar da harkokin jam’iyyar ya gaggauta gudanar da taronsu na kasa da zai bayar da damar zaben jagorori a kananan hukumomi da na jihoshi.

Wannan bukata ta su na kunshe a cikin wata sanarwa da suka fitar dauke da sa hannun gwamnan jihar Kebbi kuma shugaban kungiyar gwamnonin APC, Atiku Bagudu.

Kwamitin ya gudanar da zabukan mazabu, wanda ke cike da ce-ce-ku-ce kan zargin rashin sahihanci da kura-kurai a kwanakin baya.

Gwamnonin sun kuma bukaci likitoci masu neman kwarewa su janye yajin aikin da su ka shiga a fadin kasarnan.

Sun kuma yi kira ga mahukunta su yi kokarin daidaitawa da likitoci ganin yada yajin aiki ke tasiri ga fanin lafiya kasarnan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: