Hakumar tsaron fararen hula ta kasa sibil defens reshen jihar jigawa tace ta kama mutane 4 maza da ake zargi da haikewa wasu kananan yara 8.
Kakakin hakumar CSC Adamu Shehu ya tabbatar da kamen, yace wadanda ake zargin sun yaudari kananan yaran da kudi naira 20 ko 50 a wani kango.
Kakakin yace asirin su ya tonu bayan iyayen wadanda lamarin ke faruwa akan su sun fahimci sauyi a tattare da yaran, wanda suka sanar da hakumar. Yanzu haka dai wadanda ake zargin da ba’a bayyana sunan su ba sun shiga hannu.