Halin da ake ciki a yankin Tigray na kasar Habasha yayi muni fiye da yadda ake tsammani a baya.

0 88

Shugaban hukumar agaji ta majalisar dinkin duniya yace halin da ake ciki a yankin Tigray na kasar Habasha yayi muni fiye da yadda ake tsammani a baya.

Mark Lowcock na jawabi a jiya a wani zaman kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya.

Lowcock yace ana amfani da fyade wajen ta’addanci ga mata da kananan yara. Sojojin Eretria na amfani da yunawa a matsayin makamin yaki. Ana duka da azabtar da mutane yan gudun hijira.

Ya kara da cewa ana kashe masu aikin ceto da cin zarafinsu da hana su kai kayan agaji ga wadanda ke shan bakar wahala da fama da yunwa, tare da umartarsu akan kada su dawo. Gwamnatin Tigray ta bayar da rahoton samun mutuwar mutane sanadiyyar yunwa.

Lowcock yace binciken kwana-kwananan akan wadatar abinci a Tigray ka iya nuna ragin girman munin halin da ake ciki.

Duk da nasarar da aka samu wajen aikawa da kayan agaji zuwa yankin, Lowcock yace miliyoyin mutanen dake bukatar taimako, basa samun komai.

Leave a Reply

%d bloggers like this: