Kamar yadda BBCHausa ta wallafa “hukumar Tsaro ta Farin Kaya a Najeriya DSS, ta ƙaryata batun cewa ta janye ƙarar da take yi wa fitaccen mai shiga tsakani da masu tayar da ƙayar bayan nan, Tukur Mama.

A jiya Alhamis ne wasu kakafen yaɗa labarai suka ce DSS ta janye ƙarar da ta shigar ɗin a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, na neman ta ci gaba da tsare shi tsawon kwana 60.

Jaridar Daily Trust ta ce labarin da aka fara yaɗawan ya ce lauyan DSS A. M. Danlami, ya shaida wa Mai Shari’a Nkeonye Maha jim kaɗan cewa an janye ƙarar saboda wasu abubuwa da suka taso.

Amma a wata hira da Daily Trust ta yi da mai magana da yawun DSS Peter Afunanya, ya bayyana labarin a matsayin ƙarya ne.

Afunanya ya jaddada cewa hukumar DSS ba ta taɓa janye ƙarar Mamu da ta shigar ba, yana mai cewa ana ci gaba da shari’ar.

Tun a watan Satumba ne DSS ta kama Tukur Mamu, wanda ya suna sosai wajen shiga tsakanin masu satar mutane da dangin waɗanda aka sace.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: