Har yanzu gwamnatin tarayya na bada kuɗin tallafin man fetur – El-Rufai

0 96

Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya bayyana cewar har yanzu Gwamnatin Tarayya na biyan kuɗin tallafin man fetur.

Ya bayyana hakan ne ga manema labarai a Maiduguri, babban birnin Jihar Borno, inda ya ce Gwamnatin Tarayya na kashe maƙudan kuɗade fiye da wanda ta yi a baya a matsayin tallafin man fetur.

Idan ba a manta ba, Shugaban kasa Bola Tinubu, ya bayyana cire tallafin man fetur a jawabinsa na farko, bayan karɓar mulki a watan Mayun 2023.

Sai dai El-Rufai, ya ce yana goyon bayan cire tallafin mane fetur ɗin, inda ya bayyana cewa tsarin biyan tallafin na baya na buƙatar sauye-sauye. A cewarsa gwamnatin ta yi abin da ya dace game da cire tallafin man fetur ɗin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: