Hare-haren da ake kaiwa kan masu ibada wani yunkuri ne na haifar da kiyayyar addini a Najeriya – Kungiyar gwamnonin Arewa

0 82

Kungiyar gwamnonin Arewa ta bayyana harin da aka kai a ranar Lahadin da ta gabata a cocin darikar katolika ta Saint Francis dake Owo, jihar Ondo a matsayin wani yunkuri na haifar da kiyayyar addini.

Shugaban kungiyar kuma gwamnan jihar Filato, Simon Lalong, a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Dr Makut Maham ya fitar jiya a Jos, babban birnin jihar Filato, ya ce an kaddamar da harin ne da nufin dada rura wutar kiyayya tsakanin ‘yan Najeriya.

Simon Lalong ya bayyana goyon bayan gwamnonin ga takwaransu, Gwamna Rotimi Akeredolu da gwamnatin jihar Ondo, yana mai ba su tabbacin gudanar da addu’o’i da goyon baya a wannan lokaci na jimami.

A halin da ake ciki, kungiyar gwamnonin Najeriya, ta bayar da gudummawar naira miliyan 50 ga wadanda harin ya rutsa da su.

Shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya kuma gwamnan jihar Ekiti, Dr John Kayode Fayemi ne ya bayar da tallafin a lokacin da ya kai wa gwamna Rotimi Akeredolu ziyara a fadar gwamnatin jihar jiya a Akure, babban birnin jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: