Hon. Makki Abubakar Yalleman ya samar da ginin ajujuwa a makarantun firamare guda biyu

0 169

Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar mazabar Malam Madori da Kaugama, Honorable Makki Abubakar Yalleman, ya samar da ginin ajujuwa a makarantun firamare a Sorake dake mazabar Arki da unguwar Jama’are a mazabar Tashena.

A jawabinsa, mataimakin shugaban jam’iyyar APC na jiha, Alhaji Ango Mallam Madori, yace Makki Yalleman ya cika alkawarinsa na farko da ya dauka yayin gangamin zabe a Sorake, daya alkawarin shine samar da wutar lantarki.

Ya bukaci mutanen mazabar Mallam Madori da Kaugama da su kasance masu hakuri domin sharbar romon demokradiyya a karkashin wakilcin Makki Yalleman.

Da yake gabatar da guraren da za a yi ginin ga dan kwangila, shugaban karamar hukumar Malam Madori, Hussaini Umar BK, yace guraren ginin zasu dauki ginin ajujuwan da tebura.

Ya kara da cewa hakan cigaban kokarine na dan majalisar wajen dabbaka bangaren ilimi ta hanyar samar da tebura da litattafai da sauran kayayyakin koyo da koyarwa ga makarantu daban-daban a mazabarsa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: