Hukumar aikin Hajji ta kasa a jiya ta sanar da fara tantance kamfanonin sufurin jiragen sama da za suyi aikin jigilar alhazan bana.

0 62

Hukumar aikin Hajji ta kasa a jiya ta sanar da fara tantance kamfanonin sufurin jiragen sama da za suyi aikin jigilar alhazan bana.

An rawaito cewa akalla kamfanonin sufurin jiragen sama 7 ne suka nuna sha’awar aikin jigilar alhazan.

Kamfanonin sune na Azman Air, da Med-View Airline, da Max Air, da FlyNas, da Skypower Express, da Westlink Airlines da kuma Arik Air.

Daga cikin kamfanonin jiragen saman guda 7, shida na kasarnan ne, yayin da FlyNas ya kasance na kasar Saudiyya.

An rawaito cewa aikin tantancewar zai kasance tantance takardun kamfanonin da suka nuna sha’awa, wadanda aka tantance a shekarar 2020, biyo bayan kiran da hukumar alhazai ta bana ta yi.

Wata majiya tace tuni aka tantance kamfanonin sufurin jiragen saman a shekarar 2020 kafin a soke aikin hajji sanadiyyar barkewar annobar corona.

Leave a Reply

%d bloggers like this: