Hukumar Alhazai ta kammala jigilar maniyyanta 2,006 da ga 8:02 na safe zuwa ƙasa mai tsarki

0 162

Hukumar jindadin Alhazai ta kasa ta sanar da cewa daga karfe 8:02 na safiyar, ta kammala jigilar maniyyanta 2,006 zuwa ƙasa mai tsarki, kamar yadda ta bayyana a shafinta na X.

Wannan jigila da aka gudanar da ita da jirgin MaxAir ya tashi daga filin jirgin sama na Bauchi zuwa birnin Madina da maniyyata 384 tare da jami’i guda ɗaya.

Wannan na cikin jerin jirage biyar da suka tashi tun bayan fara jigilar a ranar Juma’ar da ta gabata, wanda ke nuna ci gaba da aiwatar da shirye-shiryen aikin Hajjin bana.

Hukumar ta ce tana ci gaba da tsara jigilar sauran maniyyata yadda ya kamata domin tabbatar da sahihancin tafiyar da kuma tsaro.

Leave a Reply