Hukumar Alhazai Ta Kasa Ta Sanar Da Wani Tsari Da Zai Bukaci Kwashe Alhazan Najeriya Da Ke Madina Zuwa Makka

0 252

Hukumar alhazai ta kasa ta sanar da wani tsari da zai bukaci kwashe alhazan Najeriya da ke Madina zuwa Makka bayan kwanaki biyar da isarsu birnin domin gudanar da aikin hajji.

Mataimakin Daraktan Yada Labarai na Hukumar, Moussa Ubandawaki, a wata sanarwa da ya fitar jiya, ya ce dokar da za ta fara aiki daga yau biyo bayan korafe-korafe akan cunkoson alhazan Najeriya a birnin Madina.

Moussa Ubandawaki ya bayyana cewa yayin da hukumar ke baiwa alhazan Najeriya daman zuwa Madina dari bisa dari a matakin farko ko kuma kafin Arafat, an dauki matakin ne don kaucewa takunkumin da aka sanyawa kasar idan aka samu cunkoson alhazai a Madina.

Ya bayyana cewa manufar ita ce a kaucewa biyan tara saboda kawo mahajjata da yawa zuwa Madina fiye da dakunan da ake da su, ko kuma a tilasta musu daukar alhazai zuwa wani wajen da bai kai matsayin wanda ake da shi na Markaziyya ba. Ya yi kira da a fahimci alhazai da jami’an aikin Hajji da sauran masu ruwa da tsaki kuma a basu goyon baya domin samun nasarar aiwatar da manufar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: