Labarai

Hukumar asusun adashen gata na fansho na jihar Jigawa ya kaddamar da biyan hakkokin ma’aikata fiye da naira miliyan 715

Hukumar asusun adashen gata na fansho na jiha da kuma kananan hukumomin jihar Jigawa, ya kaddamar da biyan hakkokin ma’aikata na kudi fiye da naira miliyan dari 715 da dubu 732.

Hakkokin ma’aikatan da za a biya sun hada da giratuti ga ma’aikatan jiha da kananan hukumomi da kuma na sashen ilmi da suka yi ritaya su 251 da hakkokin magadan ma’aikatan da suka rasu a matakin jiha da kananan hukumomi da kuma na sashen ilmi su 55 da kuma cikon kudaden fansho ga masu karbar fansho da suka rasu alhali basu cika shekaru biyar suna karbar fansho ba.

A jawabinsa wajen kaddamar da aikin biyan kudaden, sakataren zartara na asusun, Alhaji Kamilu Aliyu Musa yace daga cikin adadin kudaden za a biya giratuti ga wadanda suka yi ritaya su 251 da kudaden ya tasamma naira miliyan dari 555 da kuma hakkokin magadan ma’aikata su 55 da ya tasamma naira miliyan 155.

Kazalika za a biya cikon kudaden fansho ga masu karbar fanshon da suka rasu su 37 da kudinsu ya tasamma naira miliyan 34.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: