Labarai

Hukumar babban birnin tarayya Abuja ta sake kwashe mabarata da marasa galihu a kalla 150 saboda haddasa gurbatar muhalli da kuma bata birnin

Hukumar babban birnin tarayya Abuja, ta kwashe mabarata da marasa galihu a kalla 150 daga manyan titunan Abuja, saboda haddasa gurbatar muhalli da kuma bata birnin

Sakatariyar hukumar kula da jin dadin jama’a ta birnin tarayya, Hadiza Kabir ce ta bayyana hakan a wata sanarwa jiya a Abuja.

Kabir tace jami’ai tare da hadin gwiwar wasu hukumomin Abuja ne suka dauki nauyin kwashe mabaratan da suka hada da mata da kananan yara, ciki har da tsofaffi.

A cewarta, kwashe mutanen wani bangare ne na sabon yunkurin kawar da barace-barace a birnin, biyo bayan korafe-korafen da aka samu game da matsalar.

Ta ce wannan sabon shirin kwashe mabaratan ana tsammanin zai kwashe mabarata 400 zuwa 1,000 daga birnin biyo bayan umarnin da karamar ministar babban birnin tarayya, Ramatu Aliyu ta bayar.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: