Hukumar bada agajin gaggawa ta kasa NEMA ta karbi yan Najeriya 129 da suka makale a garin Agadez na jamhuriyar Nijar a Kano

0 82

Hukumar bada agajin gaggawa ta kasa NEMA ta karbi Yan Najeriya 129 da suka makale a garin Agadez na jamhuriyar Nijar a Kano.

Kodinetan hukumar a ofishin reshen jihar Kano Nuradeen Abdullahi ne ya bayyana hakan a lokacin da ya karbi mutanen da aka dawo da su.

Kamfanin Dillancin Labaran na kasa NAN ya bayar da rahoton cewa, mutanen da suka dawo Kano sun isa Kano ne a cikin wasu motocin alfarma guda uku da hukumar kula da kaura ta duniya ta shirya.

Ko’odinetan ya kara da cewa wadanda aka dawo da su sun hada da maza 125, Mata biyu da kuma wasu Yara kanana Biyu.

A cewarsa wadanda aka dawo da su din, sunfito ne daga sassa daban-daban na jihohin kasar nan, da suka hada da Kano, Gombe da Anambra da dai sauaransu.

Ya kara da cewa za a basu horo na tsawon kwanaki hudu domin dogaro da kai kuma za a basu tallafi domin fara sabuwar rayuwa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: