Hukumar bada agajin gaggawa ta kasa ta raba kayayyakin aikin gona ga manoma a karamar hukumar Auyo

0 60

Hukumar bada agajin gaggawa ta kasa ta raba kayayyakin aikin gona ga manoman da suka gamu da iftila`in ambaliyar ruwa a shekara ta 2020 a karamar hukumar Auyo.

Jami`in shiyya na hukumar mai kula da jihohin Kano da Jigawa, Malam Sunusi Ado shine ya bayyana hakan a lokacin kaddamar da rabon kayayyakin a Auyo.

Malam Sunusi Ado yace an rabawa manoman buhunan takin zamani da irin shukawa da maganin feshi da na`urar feshi da kuma injunan noman rani.

A jawabin da ya gabatar shugaban karamar hukumar, Auyo Alhaji Muhammad Ahmad Baffa ya yabawa gwamnatin tarayya bisa bada tallafin, inda ya bukaci wadanda suka ci gajiyar kayayyakin suyi cikakken amfani da wajen bunkasa harkokin nomansu.

A nasa jawabin shugaban kungiyar masu amfani da ruwa, Alhaji Garba Suleiman Shayi, ya godewa gwamnatin tarayya da gwamnatin jihar Jigawa saboda karfafawa manoma gwiwa wajen fuskantar harkokin nomansu.

Haka kuma ya bada tabbacin cewa manoman  zasu yi kyakykyawan amfani da kayayyakin da aka basu domin inganta al`amuran aikin gona.

Leave a Reply

%d bloggers like this: