Hukumar bunkasa ilmin addinin musulunci ta jihar Jigawa ta kaddamar da musabakar karatun Al-Qur’ani karo na 36 a Dutse.

A jawabinsa wajen bude musabakar, sakataren gwamnatin jiha, Adamu Abdulkadir Fanini ya jinjinawa gwamnati bisa daukar nauyin musabakar inda ya yi kira ga ‘yan takara da su mayar da hankali.

A jawabinsa, mai bai wa gwamna shawara kan harkokin addini, Mujitafa Sale Kwalam, ya bukaci ‘yan takara da su dauki kansu a matsayin zakaru kasancewar suna halartar musabaka a matakai daban-daban.

Ya kuma yabawa gwamnatin jiha bisa yadda take yiwa addinin musulunci hidima tare da fatan alkalan musabakar zasu kasance masu gaskiya da adalci.

A nasa jawabin shugaban hukumar gudanarwa na hukumar, Khadi Isah Gantsa, ya godewa sakataren zartarwa na hukumar bisa namijin kokarinsa wajen samun nasarar musabaka a matakai daban daban.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: