Hukumar Tsaro ta Farin Kaya wato Civil Defence ta ce ta kama wani matashi mai suna Abdulhamid Zakar, a kasuwar sayar da kayan Abinci da ke nan Hadejia bisa laifin yun kurin siyar da lalatacciyar Alkama buhu 4 wanda kudin ta ya kai Naira dubu 144.

Matashin mai shekara 23 a Duniya dan kyauyen Gatafa ne ta karamar hukumar Auyo an yanke masa hukuncin watanni 6 a gidan Yari bisa yunkurin sayar da Lalatacciyar Alkama.

Kakakin Hukumar Civil Defence na Jihar Jigawa CSC Adamu Shehu, shine ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a Dutse, inda ya ce an gabatar da mutumin ne a gaban Kotun tafi da gidan ka wanda take Hadejia bayan kamashi da laifin.

Alkalin Kotun Mai shari’a Mannir Sarki Jahun ne ya daure Matashin watanni 6 a gidan Yari bayan samun sa da laifi, wanda hakan ya sabawa Dokar sashe na 184 na Penal Code ko kuma biyan tarar Naira Dubu 70.

Haka kuma Kotu ta umarci a lalata gurbatacciyar Alkamar da aka kama.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: