Hukumar tsaron fararen hula Civil Defence ta tura jami’ai dubu 1 da 50 domin samar da tsaro a jihar Jigawa a lokacin bukukuwan Sallah.
Kakakin hukumar na jiha, Adamu Shehu, ya bayyana haka jiya a Dutse, inda ya ce kwamandan hukuamr na jiha, Musa Mala, ya bayar da tabbacin cewa jami’an da aka tura za su yi aiki tukuru.
Ya kara da cewa jami’an za su yi aiki tare da sauran jami’an tsaro wajen samar da tsaro.
Hukumar ta tabbatar wa mazauna jihar cewa za a sanya ido kan harkokin tsaro tsawon sa’o’i 24 a dukkan ranakun bukukuwan.
Adamu Shehu ya kara da cewa Musa Mala ya dorawa dukkanin kwamandojin bangarori na hukumar, da shugabanin runduna ta musamman, da kwamandojin yanki da jami’an sashe da su tabbatar da gudanar da bukukuwan lami lafiya.