Hukumar kare fararen hula da civil defence ta yi gargadi kan amfani da wuta a lokutan bukukuwan Kirsimeti da na sabuwar shekara.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a Dutse, mai dauke da sa hannun mai magana da yawun hukumar a jihar Jigawa, Adamu Shehu.

Adamu Shehu ya shawarci al’ummar jiharnan da su kara taka tsantsan da kuma kula da harkokin tsaro a yayin bukukuwan.

Ya bayyana cewa, a shirye-shiryen da ake yi na gudanar da bukukuwan Kirsimeti da na sabuwar shekara a Jihar Jigawa, Kwamandan hukumar a Jihar, Mustapha Talba, ya kuma bayar da umarnin tura jami’ai 750 cikin gaggawa domin ganin an gudanar da bukukuwan lami lafiya a fadin kananan hukumomin jiharnan 27.

Ya kuma yi kira ga al’ummar jiharnan da su kara taka tsan-tsan, su zama masu bin doka da oda, tare da kai rahoton duk wani abu bakon abu da basu yarda da shi ba, zuwa ga hukumar tsaro mafi kusa.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: