Hukumar EFCC ta kama tsohon Sakataren Gwamnatin tarayya, Mista Anyim Pium Anyim

0 86

Hukumar Yaki Da Masu Yiwa Tattalin Arzikin Kasa Zagon Kasa EFCC, ta kama tsohon Sakataren Gwamnatin tarayya Mista Anyim Pium Anyim a jiya.

Manema Labarai sun rawaito cewa Mista Anyim ya bayyana a Ofishin Hukumar ta EFCC dake Abuja a jiya da Rana.

Duk da cewa babu tabbacin gaskiyar abinda yasa EFCC ta gayyaceshi, amma wata Majiya ta tabbatar da cewa ana zargin tsohon Sakataren gwamnatin da hadin baki da tsohuwar Ministan Sufurin Jiragen Sama Mista Stella Oduah, wajen karkatar da wasu kudade.

An bayar da rahoton cewa, bincike ya gano cewa tsohon sakataren yana da Alaka da badakalar Naira Miliyan 780 wanda ake zargin Misis Stella Oduah da hannu a ciki.

Sanata Stella Oduah wanda a yanzu ita ce take wakiltar Anambra ta Arewa, ana zargin cewa ta mallaki kadarori 4 a birnin London a lokacin da take Minista.

Leave a Reply

%d bloggers like this: