Hukumar Fanson Ma’aikata ta jihar Jigawa ta ce ta biya Naira miliyan 181 ga iyalan ma’aikata 72 wanda suka rasu suna aiki

0 92

Hukumar Fanson Ma’aikata ta Jihar Jigawa ta ce ta biya Naira Miliyan 181 ga Iyalan Ma’aikata 72 wanda suka rasu suna aiki cikin watanni 2 da suka gabata a fadin Jihar nan.

Sakataren Zartarwa na Hukumar Alhaji Kamilu Aliyu Musa, shine ya bayyana hakan jiya a lokacin da ya ke biyan hakkokin Ma’aikata 375 wanda suka yi Ritaya a aikin Gwamnati.

A cewarsa, hukumar ta biya Naira Miliyan 783 da dubu 734 ga Ma’aikata 375 da suka yi Ritaya a aikin Gwamnatin Jihar.

Alhaji Kamilu, ya ce kudaden na mutanen da suka yi Ritaya a aikin Gwamnati ne daga watan Yuli zuwa Satumba na wannan shekarar ne.

Haka kuma ya ce kudaden sun kunshi na wanda suka yi Ritaya da wadda suka rasu suna bakin aiki a matakai daban-daban.

Shugaban Hukumar ya ce kudaden sun kunshi na Ma’aikatan Jiha da na Ma’aikatan Sashen Ilimi na Karamar Hukuma da kuma na Sashen Mulki.

Kazalika, ya yabawa Gwamna Muhammad Badaru Abubakar, bisa Namijin kokarin sa, wajen biyan hakkokin Ma’aikatan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: