Hukumar hana fasa ƙwauri ta kwastan tace jami’anta sun kama magunguna a jihar Katsina da kudinsu ya kama sama da naira miliyan 110

0 77

Hukumar hana fasa kwauri ta kwastan tace jami’anta sun kama magunguna da sauran abubuwa a yankin jihar Katsina da kudinsu ya kama sama da naira miliyan 110.

Jagoran hukumar na shiyyar B, Useni Aliyu, wanda ya sanar da haka jiya a Katsina lokacin da yake jawabi ga manema labarai yace an yi kamenne daga ranar ga 2 watan Oktoba zuwa yanzu.

Yace hukumar ta kama katan 12 na kwayoyi daban-daban dauke da lambar NAFDAC ta bogi, wadanda kudinsu ya kama sama da naira miliyan 6, tare da wani babur na naira dubu 60.

Ya kara da cewa a cikin makonnin, hukumar ta kama buhunan shinkafa ‘yar kasar waje mai nauyin kilo 50 guda 450.

Hukumar ta kama wasu buhunan shinkafar ‘yar kasar waje mai nauyin kilo 25 guda 100, da katan 300 na taliya.

Ya kara da cewa jami’an hukumar sun kuma samu nasarar kama katan 790 na sabulun wanka dan kasar waje.

Leave a Reply

%d bloggers like this: