Hukumar Hisbah ta Jihar Jigawa ta kama tare da kwace wasu kwalaban giiya 1,426 a kananan hukumomi 2 dake jihar jigawa.

Kwamandan hukumar na jihar Jigawa Malam Ibrahim Dahiru ne ya bayyana hakan a lokacin dayake zantawa da kamfanin dillacin labarai na kasa NAN a ranar Alhamis a Dutse.

Malam Dahiru ya kuma kara da cewa, sun kama wata Jarkar mai cin Lita 25 a cike da giya yar cikin gida da akafi sani da suna Burukutu.

Ya kara da cewa sun kama kwalaban giyan ne a lokacin da jami’an hukumar suka kai farmaki a wasu Otel, da wasu mashayu dake kananan hukumomi 2, tare da kama wasu mutane 15, ciki harda wata Mace.

Malam Dahiru ya kuma tabbatar da cewa tini suka mika wadanda ake zargin ga hukumar yan sanda domin zurfafa bincike.

Ya kuma shawarci al’umma akan su kasance masu bin doka da oda, musamman akan siya da kuma shan giya a jihar Jigawa.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: