

- Wasu ‘yan bindiga sun kashe wakilai uku na ‘yan takarar gwamna na jam’iyyar PDP daga karamar hukumar Mariga ta jihar Neja - May 26, 2022
- Dalilan da yasa wasu ‘yan takarar gwamna 2 na jam’iyyar APC suka yi watsi da zaman ganawar da gwamna Badaru ya kira domin a samar da dan takarar daya tal - May 26, 2022
- Mataimakin kwamishinan ‘yan sandan da aka dakatar, Abba Kyari ya garzaya wata babbar kotun tarayya domin neman belinsa - May 26, 2022
Hukumar Hizbah a jihar Jigawa ta sanar da cewa ta kashe auren dole guda 330 da aka gudanar a shekarar 2019 bayan amaren sun gudu daga gidajen auren nasu.
Shugaban hukumar Ustaz Ibrahim Garki ne ya bayyanawa manema labarai cewa sun kashe auren dolen ne bayan amaren sun kai ƙara ofishohin Hizbah dake jihar.

Ya ce bayan kashe auren, hukumar ta mayar da amaren gidan iyayensu.
Haka zalika hukumar ta baiwa iyayen waɗanda aka kashewa auren shawara su sanya zawaran a makaranta, saboda yawancin yan matan da aka kashewa auren dolen kananan yara ne.
A ƙarshe ya ce hukumar Hizbar ta samu nasarar dakile wasu auren dolen da aka shirya tun kafin a kai ga yinsu.