Hukumar ilimi matakin farko ta jihar Jigawa ta yi bikin bude bada tayin kwangilar gina azuzuwa 180

0 57

Hukumar ilimi matakin farko ta jihar Jigawa ta yi bikin bude bada tayin kwangilar gina azuzuwa 180 da kuma gyaran wadanda suka lalace 288 a wasu daga cikin makarantun jihar nan.

A jawabinsa wajen bikin bude bayar da tayin kwangilar wakili a Hukumar, Alhaji Nuhu Muhammad wanda ya wakilci sakataren zartarwa na hukumar, ya ce ayyuka na hadin gwiwa tsakanin hukumar ilimi matakin farko ta jiha da kuma hukumar ilimin bai daya.

Ya ce bisa kwarin gwiwa da suke samu daga Gwamna Badaru Abubakar, sun cimma nasarori da dama, inda ya bukaci duk kamfanin da ya yi nasarar samun kwangilar da ya gudanar da aiki mai inganci.

A jawabinsa daraktan ayyuka na hukumar, Architech Hussaini Suleiman, ya ce tuni aka saki naira miliyan 946 domin gina azuzuwa 180 da gyaran wasu 288 da gina kananan bandakuna da famfuna 56 da samar da kujeru da kuma gadajen kwanciya na dalibai.

Leave a Reply

%d bloggers like this: