Hukumar INEC ta bayyana aniyarta na fara amfani da fasahar AI wajen gudanar da zaɓen Najeriya

0 201

Hukumar zaɓe ta kasa, INEC ta bayyana aniyarta na fara amfani da fasahar ƙirƙirarriyar basira ta AI wajen gudanar da ayyukan zaɓe a zamanance.

Cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar ta hannun babban kwamishininta kuma shugaban kwamitin wayar da kai da yaɗa labarai, Sam Olumekun, ta ce hukumar fasahar za ta taimaka wajen sauƙaƙa wa hukumar ɗaukar matakai la’akari da bayanan da za ta samu ta hanyar fasahar.

A cewar sanarwar, fasahar za ta ƙara ƙarfafa sahihancin zaɓuka ta hanyar tattara alƙaluma da kuma tantance aihinin alƙaluman zaɓe.

Tuni dai hukumar ta sanar da kafa sashen fasahar ƙirƙirarriyar basirar ta AI a ƙarƙashin ɓangaren sadarwar hukumar, domin fara inganta ayyukan fasaha na hukumar, tare da kawar da matsalolin da ake fuskanta da suka shafi fasahar sadarwa.

Haka kuma hakumar tace amfani da fasahar ta AI zata inganta harkokin rarraba kayayyakin zabe izuwa rumfunan zabe. Hukumar ta ce a baya-bayan nan ta halarci tarukan duniya waɗanda ta ce an shirya kan tasirin fasahar AI kan zaɓukan ƙasashe.

Leave a Reply