Labarai

Hukumar INEC ta bayyana Bashir Machina a matsayin tabbataccen wanda ya lashe zaben fidda gwani na takarar sanata a yankin Yobe ta Arewa da jam’iyyar APC ta gudanar

An bayyana Bashir Machina a matsayin tabbataccen wanda ya lashe zaben fidda gwani na takarar sanata a yankin Yobe ta rewa da jam’iyyar APC ta gudanar.

Hakumar zabe mai zaman kanta kasa INEC itace ta bada wannan tabbaci.

sawabaFm ta rawaito yadda Bashir machina ya lashe zaben sanatan yobe ta arewan a karkashin jam’iyyar APC, bayan ya samu kuri’u 289 daga ciki kuri’u 300 da aka kada, wanda daga baya shugaban majalisar dattawa sanata Ahmed Lawan ke ikirarin shine dan takarar.

Haka kuma INEC ta bayyana Bashir Machina a matsayin wanda ya lashe zaben, sai dai nasarar har yanzu bata samu ba, yayin da yake ake tinanin zai fafata da sauran yan takarkaru daga wasu jam’iyyyun a babban zaben 2023.

Idan dai za’a iya tinawa Sanata Ahmed lawan yayi yunkurin kwace takarar sanatan daga wajen Machina bayan yasha kaye zaben fidda gwani na dan takarar shugaban kasa a babban taron jam’iyyar APC da akayi a ranar 8 ga watan da muke ciki, wanda Bola Ahmed Tinubu ya lashe.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: