Hukumar INEC ta ce ta soke rajistar mutum miliyan 2 da dubu 700 waɗanda aka gano sun yi rajistar fiye da sau ɗaya

0 141

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa, INEC, ta ce ta soke rajistar mutum miliyan 2 da dubu 700 waɗanda aka gano sun yi rajistar fiye da sau ɗaya.

Shugaban hukumar Farfesa Mahmoud Yakubu ne ya bayyana haka a wani taron tataunawa kan mulkin demokraɗiyya da ya gudana a birnin Washington DC na ƙasar Amurka.

A cikin bayanin da ya yi, shugaban hukumar ta INEC, ya ce nan da watan Nuwamba mutane za su iya karɓar sabbin katunan zaɓen nasu.

Ya ce yanzu haka ma an kammala haɗa kashi 50 na katunan zaɓen.

Sai dai a cewar sa wata babbar matsalar da ke damun hukumar ita ce rashin tsaro a faɗin kasa.

Ya ce hukumar tana sanya ido kan musamman abubuwan da ke faruwa a arewa-maso-yammaci da kuma kudu-maso-gabacin kasa.

Sai dai a cewarsa hukumar ta INEC ta gana da shugabanni a bangaren tsaro, waɗanda suka tabbatar da cewar lamurra za su gyaru kafin lokacin zaɓen.

Leave a Reply

%d bloggers like this: