Hukumar INEC ta ware Naira biliyan 4 da Miliyan 200 domin cigaba da yin aikin katunan zabe domin sake shirin zaben shekarar 2023

0 66

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa INEC ta ware Naira Biliyan 4 da Miliyan 200 domin cigaba da yin aikin katunan zabe domin sake shirin zaben shekarar 2023.

Shugaban Hukumar na Kasa Farfesa Mahmoud Yakubu, shine ya bayyana hakan a lokacin da ya bayyana a gaban Kwamatin Zabe na Hadakar Majalisun Kasa domin kare kasafin kudin Hukumar na shekarar 2022.

Da yake bayyana Jadawalin kasafin kudin hukumar na shekarar 2022 na Naira Biliyan 140 Farfesa Mahmoud Yakubu, ya fadawa kwamatin cewa Naira Biliyan 100 da aka warewar hukumar yayi kadan, domin gudanar da zaben shekarar 2023 ciki harda zaben Gwamnonin Jihohin Ekiti da Osun.

Haka kuma ya ce hukumar ta ware Naira Biliyan 7 domin gudanar da zaben gwamna a Jihohin Ekiti da Osun.

Leave a Reply

%d bloggers like this: