Hukumar INEC tana shirin fitar da sabbin ƙa’idoji da za su fayyace yadda za a duba sakamakon zaɓen 2027

0 130

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta ce tana shirin fitar da sabbin ƙa’idoji da za su fayyace yadda za a duba sakamakon zaɓe da aka bayyana, gabanin babban zaɓen 2027.

Shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu, ya bayyana haka yayin taron koli da kwamishinonin zaɓe na jihohi a Abuja, yana mai cewa hakan na da nasaba da rashin fahimta kan sashe na 65 na dokar zaɓe ta 2022.

Sabbin ƙa’idojin za su taimaka wajen kara gaskiya da bayyananniyar hanya wajen tattara sakamakon zaɓe.

Ya kuma ce ana ci gaba da tuntubar jam’iyyun siyasa, kungiyoyin fararen hula da hukumomin tsaro don inganta tsarin zaɓe.

Leave a Reply