Hukumar jami’ar Bayero dake Kano ta amince da karawa malaman makarantar da ma’aikatanta da basa koyarwa matsayi su 772

0 310

Hukumar jami’ar Bayero dake Kano ta amince da karawa malaman makarantar da ma’aikatanta da basa koyarwa matsayi su 772.

Jami’ar ta bayyana hakan ne ta bakin Sakataren yada labarai na jami’ar Mr. Lamara Garba, wanda ya fitar da sanarwar ga manema labarai a birnin Kano.

Sanarwar tace, andaga likafar wasu malamai 7 wadanda yanzu haka suka zama Farfesa, sai malamai 18 da suke matakin zama Farfesas, sai kuma wasu ma’aikatan jami’an da basa koyarwa su 747 da aka karawa matsayi.

Ya kara da cewa akwai wasu manyan ma’aikata 3 da aka mayar dasu zuwa matsayin mataimakan rijistra.

Cikin sanar da Lamara ya fitar, ta kuma kara da cewa, wadanda aka mayar da su ferfesa da mataimakan farfesas, sun samu wannan karin girman ne tin a ranar 1 ga watan Oktoba na 2020.

Haka kuma ma’aikatan jami’ar da basa koyarwa, sun samu karin girma ne tin ranar 1 ga watan Oktoba na 2021.

Anasa bangaren shugaban jami’ar ya bukaci sabbin ma’aikatan da aka karawa girma akan su kasance masu jajircewa a ayyukansu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: