Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Jigawa ta kammala jigilar rukuni na biyu, wanda shi ne na ƙarshe, na maniyyata 368 zuwa ƙasa mai tsarki domin gudanar da aikin hajjin shekarar 2025.
Tun a ranar Litinin ne hukumar ta fara jigilar maniyyata inda aka tashi da rukuni na farko na maniyyata 550 daga filin jirgin sama na Nuhu Muhammadu Sunusi da ke Dutse, babban birnin jihar.
Wannan rukuni na ƙarshe ya ƙunshi maniyyata daga ƙananan hukumomin Taura, Buji da Birnin Kudu, kuma an tashi da su ne da safiyar Alhamis da jirgin Max Air Boeing 747, a daidai ƙarfe 01:51 na dare agogon Najeriya.
A cikin saƙon ban kwana da ya aike musu, Gwamna Umar Namadi ya shawarce su da su kasance wakilan kirki na Najeriya a ƙasa mai tsarki, tare da nuna ɗabi’a ta gari da kuma yi wa jihar da ƙasar addu’ar zaman lafiya da cigaba. Daraktan hukumar, Ahmed Umar Labbo, ya tabbatar wa da maniyyatan cewa za a ba su cikakken kulawa da kyakkyawar hidima a lokacin ziyarar su ta hajji.